September 18, 2026

An Fara Binciken Kisan Da Sojoji Suka Yima Dansanda a Jihar Lagos.

0

Sojojin dake aiki da runduna ta 81 sun yi wa wani dan sanda duka har lahira a unguwar Ojo dake jihar Lagos.

Mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na shiyya ta 81, Manjo Olaniyi Osoba, ya tabbatar da faruwar lamarin a yauJuma’a, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar DailyTrust.

“An jawo hankalin rundunar ta 81 ne akan wani labari dake yawo kan yanar gizo dangane da abinda ya faru tsakanin wasu sojoji da ‘yan sanda a kusa da Ojo a Lagos da ya yi sanadin rasa ran dan sanda,” inji Manjo Osoba a cikin wata sanarwa da ya fitar.

“Tuni rundunar ta fara ganawa da rundunar ‘yan sandan jihar Lagos domin warware matsalar. Akwai matukar takaici akan wannan lamari duba da yadda rundunar bata san rashin da’a. “

A cewar sa, sashen ya kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan lamarin.

Ya kara da cewa “A karshen binciken, duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.”

“Saboda haka, rundunar sojin ta mika ta’aziyya ga rundunar ‘yan sandan da kuma iyalan mamacin.”

Shi ma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Lagos SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce “suna aiki tare da hukumomin sojojin Najeriya don daidaita lamarin; su amso jami’insu, bindigarshi da kuma harsasai,” kamar yadda ya bayyana a shafinsa ma Tweeter yau Juma’a.

A daidai lokacin da hukumomin yan sanda dana soji ba su ce komai ba, an ta bayyana cewa sojojin na kan hanyarsu ta zuwa wani aikin a sansanin soji dake Ojo a ranar Laraba a lokacin da lamarin ya faru.

Sojojin dake cikin motar safa, an bada rohoton cewa cunkosan ababen hawan ya tare masu hanya kusa da kasuwar duniya dake babbar hanyar Badagry a Lagos. A lokacin da suka lura cewa yan sandan suka haddasa cunkosan dake kan hanyar da ya tare masu mota, sai sojojin suka sauko kasa suka farma yan sandan.

Hakan ya haifar da zazzafar cece-kuce da sojojin da aka ce sun kai wasu daga cikin jami’an ‘yan sandan zuwa bariki, inda suka kai su bariki suka bige su wanda ya yi sanadin mutuwar daya daga cikinsu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *