September 17, 2026

Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Hon. Mansur Baure Ya Yabawa Matakin Da Gwamna Radda Ya Ɗauka.

0

Jigo a jam’iyyar APC ta ƙaramar hukumar Ƙanƙara Honarabul Mansur Ɓaure ya yabawa gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa bisa kalaman gwamnan da ya ce ba zai naɗa Kantomomi ba a shugabancin ƙananan hukumomi a Katsina.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya a wani taron masu ruwa da tsaki, Gwamna Raɗɗa ya tabbatar da cewar ko kaɗan ba zai yi kantomomi ba sai dai zai gudanar da zaɓe a ƙarshen wa’adin mulkin shugabannin Kananan Hukumomin da ke ci a yanzu.

Hon. Mansur ya yi waɗannan Kalamai ne a ya yin da yake zantawa da manema labarai a Katsina inda ya ce wannan wani sabon al’amari ne d ba a saba da shi a wannan jiha ta Katsina

Hon. Mansur Baure na daga cikin waɗanda lamarin ya yi wa dadi inda ya jinjinawa Gwamnan kan wannan kuduri nasa na farfaɗo da harkokin demokraɗiyya a Ƙananan Hukumomi.

Haka kuma, Baure yace gudanar da zaɓen zai ba kowa damar zaɓen wanda ya keso ba tare da an yi ɗauki ɗora ba kamar yadda ta faru a can baya ba.

Sai dai kuma, Baure ya shawarci mutane da su yi amfani da wannan dama wajen fitar da mutane sahihai kuma nagartattu da su ke zaune a cikin su kuma su ka san matsalolin su.

” Ina kira da mutane su sanya natsuwa su duba cancanta tare da yin amfani da ma’aunin gaskiya wajen fitar da ‘yan takara domin gudun kar a koma yar gidan jiya a wasu Kananan Hukumomin”, Baure ya Kara da cewa.

Daga ƙarshe ya miƙa saƙon taya Murna ga tsohon mataimakin shugaban majalisar dokoki ta jihar Katsina Hon. Ɗalhatu Shehu Tafoki bisa nasarar da ya samu ta zamowa ɗan Majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Kankara/Faskari da Sabuwa a zaɓen cike gurbi da ya gudana a kwanakin baya.

A cewarsa ” Nasarar Tafoki nasarar mataimakin Gwamnan Jihar Katsina ce Mal. Faruk Lawal Jobe Kuma nasarar Sanata. Muntari Ɗandutse ce da dukkan sauran masu ruwa da tsaki na Yankin Funtua”

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *