Gwamnatin jihar Katsina Zata Kashe Naira Biliyan 16.7 wajen Sayan Takin Zamani ga Manoma
Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ta amince da ware kudi har naira miliyan dubu sha shida da ɗari bakwai domin sayen takin zamani da za a rabawa manoma a jihar.
Kwamishinan ayyukan gona na jihar Katsina, Farfesa Ahmad Bakori ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwa a gidan gwamnatin jihar Katsina
Da yake yin bayani dalla-dalla Farfesa Ahmad Bakori ya ce ton dubu 20 na takin zamani zai kasance samfurin urea ton dubu shida sai kuma samfurin NPK 15-15 da NPK 10-10 ton dubu goma.
A cewar sa, harkar noma da samar da wadataccen abinci na daga cikin bangarorin da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya sanya a cikin mahimman abubuwa a gwamnatin sa.
Idan za a yi tunawa jihar Katsina na ɗaya daga cikin jahohin arewa maso yamma da suke samar da kaso mafi tsoka a bangaren noma.
Sai dai jihar da kuma yankin na fuskantar ƙalubalen tsaro shekara da shekaru wanda hakan tasa yanzu ba a iya noma rabin abinda ake noma ada.
Shin ko wannan ƙoƙari na gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa zai taimaka wajen farfaɗo da harkokin noma da kiwo a wannan jiha ta Katsina, lokaci ne zai nuna.
