Zaɓan 2023: Hon. Sani Aliyu Ɗanlami Na Cigaba Da Samun Karɓuwa A Katsina Ta Tsakiya. Bincike
A wannan kakar zaɓe mai kaɗawa ta 2023 tauraron ɗan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya Hon. Sani Aliyu Ɗanlami na cigaba da haskaka wa a tsakanin ‘yan takara.
Wani bincike mai zaman kansa da wannan kafa ta Popular News Hausa ta gudanar ta gano cewa Hon. Sani Ɗanlami na cigaba da samun karɓuwa da tagomashi a wajan magoya baya da masoya.
Haka kuma yana daga cikin ‘yan takarar majalisar tarayya a jihar Katsina da suke cigaba da shiga lungu da sako domin neman alfarmar al’umma akan wannan zaɓe mai zuwa.
” Gaskiya yanzu iskan nan mai kaɗawa babu wani ɗan takara daga kowace jami’yya da ke samun karɓuwa a wajan al’umma kamar Hon Sani Ɗanlami, kuma duk Jam’iyyun nan PDP da APC suna son shi, sannan suna yi masa yaki a madadinsa ‘ inji wani ɗan PDP
Ya cigaba da cewa Hon. Sani Aliyu Ɗanlami wani mutum ne na musamman a cikin ‘yan siyasar wannan zamani, saboda suke yi mashi fatan nasara a wannan takara da yake yi.
Wani abu da wannan bincike ya gano shi ne, Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya ƙara gyara mu’amulolinsa da jama’a saɓanin baya da wasu ke ganin kamar ya canza saboda dalilan siyasa.
Kazalika Hon. Sani Aliyu Ɗanlami da gaske yake yi akan maganar takarar kuma ya shirya domin tunkarar kowane irin ƙalubale da ya shafi takarar majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya.
Duba da yadda jam’iyyar APC ke fuskantar turjiya daga wasu ‘ya ‘yan ta da kuma ‘yan adawa, amma hakan bai hana haskawar tauraron Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ba a cikin birnin Katsina.
Kamar yadda kowa ya sani Hon. Sani Aliyu Ɗanlami yana ɗaya daga mutane ƙalilan da suke kare mutuncin gwamna Aminu Bello Masari a kowane mataki, yanzu haka yana nan akan wannan matsayi.
Sai dai kuma bincike na mu ya gano cewa duba da halin wasu ‘yan takarar jam’iyyar APC da Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ke fatan ganin sun samu nasara baki ɗaya, na iya zama wani ƙalubale wajen shi, saboda mugun halin da kuma halin ‘yan dambe da suke fama da shi.
Binciken ya tabbatar da cewa dagewar Hon. Sani Aliyu Ɗanlami akan zaɓan ‘yan takarar kan iya zama matsala a wajensa saboda shi yana san nasarar jami’yyar APC tun daga ƙasa har sama abinda wasu ke ganin da wahala auren gurguwa nesa, sun fi kallon cewa shi dai kam akwai kyakkyawar fatan zai kai ga nasara, amma sauran sai abinda lokaci ya nuna…!
Daga karshe binciken ya samu tabbacin akwai wasu na tare da shi da ke buƙatar lura da yadda suke tafiyar da al’amuran sa domin gudun tara masa makiya maimakon masoya
