September 18, 2026

Ganduje Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Karshe A Gaban Zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano

0

Daga Babangida Sunusi, Kano

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Ganduje, ya gabatar da kasafin baɗi da ya kai kimanin naira biliyan dari biyu da arba’in da biyar,ga zauren majalisar dokokin jihar kano domin dubawa tare da sahile masa yin amfani da shi.

Ganduje, ya gabatar da kasafin ne a yau Juma’a.a yayin da yake jawabinsa lokacin gabatar da kasafin, gwamnan ya ce, taken kasafin shi ne “Ɗorawa kan ayyukan ci gaba Karo na biyu”.

Haka kuma Ganduje ya ce, kasafin zai ƙarfafa tare da inganta rayuwar al’ummar jihar Kano la’akari da tanade-tanade da ke cikinsa.

Sannan ya kara da cewa, kasafin ya ƙunshi naira biliyan 144 da za a kashe wajen yin manyan ayyuka watau kimanin kashi 59 bisa 100 na kasafin, sai kuma naira biliyan 100 na kuɗaɗen da ake kashewa akai-akai.

Ya kuma nanata cewa a kasafin, an ware wa fannin lafiya Naira biliyan 39.1,sai albarkatun ruwa Naira biliyan 15,fannin sufuri Naira biliyan 8.6, haka Kuma fannin noma Naira biliyan 19.9 yayin da ayyuka da ababen more rayuwa suka samu Naira biliyan 35, inji shi.

Gwamnan ya ce bangaren ilimi ya samu kaso mafi girma na kasafin kudi da Naira biliyan 62, wanda ya kai kashi 27 cikin 100 fiye da shawarar UNESCO da Majalisar Dinkin Duniya.

Ya Kara da cewar za a fitar da kudaden ne wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsare da nufin tabbatar da ingantaccen ilimi a dukkan matakan da suka dace.

Inda ya cigaba da fadar cewa za’a kuma yi amfani da wani bangare na kudaden wajen inganta shirin ilimi kyauta kuma dole da gwamnatin ta samar a jihar.

A jawabinsa bayan gabatar da kasafin, Shugaban majalisar dokoki Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya bai wa gwamnan tabbacin yin gaggauwar sahale kasafin da zarar sun kammala aikin a kansa.

Haka kuma Chidari, ya bukaci ma’aikatun gwamnati da hukumomi da su kasance cikin shiri don kare kasafin a zauren majalisar, kazalika daga lokacin da karbi ragamar jagoran cin majalisar matsayin shugaba ya samu sahile kuduri guda 44 daban daban.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *