Yadda Taron Ƙarawa Juna Sani Da Hukumar Kidaya Ta Ƙasa Ta Shirya A Katsina
Hukumar kidaya ta ƙasa reshen jihar Katsina ta shirya taron bita akan yadda aikin kidayar na shekarar 2023 zai kasance a hukumance.
Da yake gabatar da jawabi kwamishinan kidaya na ƙasa injiniya Bala Almu Banye ya ce an shirya wannan taro ne domin baje kolin yadda za a gudanar da kidayar a matakin gudumumi.
Ya kara da cewa sun shirya raba Alƙaluman yadda suka shata gudumumi a wannan kidayar da za a yi a shekarar 2023.
Ya ce da cikin abubuwan da suka tanadar sun haɗa da yawan makarantu da hanyoyi da gidaje da asibitoci da kasuwanni duk acikin kudin ajiyar bayanai da suka tattara sannan za su fitar da taswirar mazaɓa da unguwanni da kananan hukumomi da jahohi baƙi ɗaya.
Shima da yake gabatar da jawabinsa
Daraktan Hukumar na kasa, Alh. Hadi Yahaya yayi kira ga masu ruwa da tsaki na kananan hukumomi da su lura da yawan jama’ar su domin akwai adadin da ake so ko wacce karamar hukuma ta kai wanda ake son a kalla mutum dubu dari biyuda hamsin (250) kamar yadda tsarin kundin mulkin ƙasa ya tanada.
A nashi jawabin kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar Katsina, Hon Yau Umar Gwajo-gwajo ya ce wannan aiki ne da yake da matuƙar mahimmanci wanda ya ce ta wannan hanyar ce ake rabon arzikin ƙasa.
Hon. Yau Umar Gwajo-gwajo wanda ya samu wakilcin daraktan mulki na ma’aikatar, Lawal Attahiru Bakori ya ce lallai ma’aikatar ƙananan hukumomi da Masarautu ta jihar Katsina a shirye take wajan bada duk wata gudunmawa da ake bukata domin samun nasarar wannan aiki
Haka shima a nashi ta’aliki shugaban ƙaramar hukumar Kaita kuma shugaban kungiyar shuwagabannin ƙananan hukumomi (ALGON) injiniya Bello Lawal ‘Yandaki ya ce sun shirya tsaf domin bada duk wata gudunmawa da ake buƙata wajan samun nasarar aikin kidayar shekarar 2023.
A ya yin da ake taron an baiwa shugabannin kananan hukumomi taswirar kananan hukumominsu a cikin ma’adani na na’ura mai kwakwalwa ‘Flash Drive’ domin dubawa da tantancewa.
