September 18, 2026

Akwai Buƙatar EFCC Saboda Wasu Zarge-Zarge A Katsina. Cewar Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula

0

Shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula na jihar Katsina, Abdurrahman Dutsin-ma ya yi kira ga hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa watau EFCC ta bude ofishin ta a jihar Katsina.

Abdulrahman Dutsin-ma ya yi wannan kiran ne da yake jawabi a wurin wani taron bita da jami’an hukumar ta shirya ma kungiyoyin fararen hula na jihar Katsina kan yadda za su taimaka wurin yakin da fasa kwabrin kudade ta hanyar yin rijista da hukumar a bangaren da ta ware.

Haka zalika shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hular ya tabbatar ma hukumar EFCC cewa al’ummar jihar Katsina suna da matukar bukatar hukumar a jihar domin kuwa akwai zarge zarge da dama na almundahana da cin hanci da rashawa da ke gudana a jihar wadanda kuma suke bukatar bincike.

Daga karshe, Abdulrahman Dutsin-ma ya tabbatar ma jami’an hukumar ta EFCC cewa za su cigaba da yin iya bakin kokarin su wajen taimakon hukumar wajen gudanar da ayyukan ta da kundin tsarin mulki ya ba ta.

Tun da farko dai jami’in hukumar ta EFCC wanda ya jagoranci sauran ma’aikatan hukumar, Mista Francis Bassey, daga sashen hukumar na musamman dake sa ido a kan masu safara da fasa kwaurin kudade watau (Special Control Unit Against Money Laundering, SCUML) a hedikwatar hukumar hukumar dake Kano ya bayyana cewa sun zo ne jihar Katsina domin su yi ma kungiyoyin fararen hular jihar bita kan sabbin ka’idoji da dokoki na hukumar musamman kan yadda za su yi rijistar asusun ajiyar bankin su da hukumar.

A yayin taron bitar, kungiyoyin fararen hular sun yi tambayoyi kan abun da ya shige masu duhu bayan jami’an hukumar sun gama masu lakcocin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *