‘Yan Ta’adda Sun Kashe Matafiya 6 A Wani Sabon Hari Da Aka Kai A Borno.
‘Yan ta’addan na ISWAP dai sun kashe akalla fararen hula shida a wani harin kwantan bauna da suka kai kan babbar a hanyar Dikwa zuwa Ngala na jihar Borno ranar Asabar.
Majiyar Popular News Hausa ta LEADERSHIP ta ruwaito cewa, hanyar Dikwa zuwa Ngala ita ce hanyar da ta hada babban birnin jihar Borno da karamar hukumar Dikwa da Ngala, kuma hanyoyin jigilar kayayyaki ne zuwa wasu kasashe makwabta na Afirka kamar Chadi, Kamaru da dai sauransu.
A cewar wani rahoton sirri da Zagazola Makama kwararre kan yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi ya samu daga majiyoyin soji, ya bayyanawa wakilin LEADERSHIP cewa, an kashe mutanen ne bayan da ‘yan ta’addan suka bude masu wuta.
Majiyar ta kara da cewa, wasu fararen hula biyu sun samu raunukan harbin bindiga.
“Bayan haka, sun yi awon gaba da motar yan kasuwa guda daya, tare da kona motocin gida guda hudu, da motocin yan kasuwa guda biyu, da babbar motar da ba kowa a ciki, da kuma dabbobi,” in ji majiyar.
Majiyar ta kara da cewa wata motar daukar kaya guda ta taka wani abu da aka ɗana a hanyar yayin da take kokarin komawa baya da ta hango yan ta’addan.
”Kuma ƴan ta’addan sun gudu bayan da suka sojin Najeriya,” in ji majiyar.
