Yan Bindiga Sun Kai Hari Cocin Kaduna, Tare Da Kashe Mutane 3.
Yan bindigar sun kai farmakin ne a cocin Maranatha Baptist da kuma cocin St. Moses Catholic dake kauyen Rubu cikin Kajuru a yau Lahadi, inda suka kashe mutane uku.
Wadanda aka kashen sun hada da Peter Madaki shugaban Ungwan Fada, Elisha Ezekiel, Mazaunin Ungwan Fada da Ali Zamani shugaban matasan Rubu.
Majiyar Popular News Hausa ta jaridar DailyTrust ta bada rohoton cewa, an jikkata mutane 2, tare da yin garkuwa da mutanen da har yanzu ba a san adadinsu ba a yankin.
Yan bindigar sun zo ne a kan babura suka far wa mutanen jim kadan bayan rufe cocin.
Al’ummomin biyu da aka kai ma harin na cikin kauyen Rubu ne. Kuma hakimin unguwar Anguwar Fada na cikin wadanda aka kashe,” in ji wani Maigari.
Ya bayyana cewa sauran masu ibadar sun tsere ne ta cikin daji dake kusa da wurin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan tsaro na cikin gida Samuel Aruwan, ya ce maharan sun fara ayyukansu ne daga Ungwar Fada, inda suka shiga Ungwar Turawa, kafin daga bisani su shiga Ungwar Makama, daga nan sai kauyen Rubu.
Ya bayyana cewa yan ta’addan sun kwashe kayayyakin shagunan mutane masu daraja daga kauyukan.
Aruwan ya ce, “A bin bakin ciki, jami’an tsaro sun kai rahoto ga gwamnatin jihar Kaduna cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan masu ibada da mazauna unguwannin Ungwar Fada, Ungwar Tarawa, da Ungwan Makama dake yankin Rubu cikin karamar hukumar Kajuru.
“Da take karbar rahoton, mukaddashin gwamnan jihar, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta bayyana matukar bakin ciki tare da yin Allah wadai da harin da kakkausar murya. Ta kuma mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda aka kashe, yayin da ta yi addu’ar Allah ya jikan su.”
Aruwan ya dai ce ana gudanar da sintiri na tsaro a yankin yayin da ake ci gaba da bincike.
