November 17, 2026

An Sace Tsohon Sakatare Janar Na NFF.

0

An yi garkuwa da tsohon sakatare janar na hukumar kwallon kafar Najeriya NFF Sani Toro akan hanyar sa ta zuwa jihar Bauchi daga Abuja.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili, yayin da yake tabbatar da yin garkuwa da shi, ya ce bai da cikakken bayani kan lamarin, domin ya faru a wajen jiharsa.

Majiyar jaridar Popular News Hausa ta jaridarLEADERSHIP ta bada labarin cewa, an yi garkuwa da tsohon sakatare janar na hukumar kwallon kafar ne tare da wani tsohon mataimakin kocin Super Eagles, Garba Yila.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *