September 18, 2026

Harin Cocin Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Nemi Kudin Fansa Naira Miliyan 100.

0

Yan bindiga da suka kai hari cocin Maranatha Baptist da cocin St Moses Catholic da ke Robuh, Ungwar Aku cikin karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna Lahadin da ta gabata, sun nemi kudin fansa naira miliyan 100 don sakin masu ibada kusan 36 da ke hannunsu.

Kwamishinan tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan a ranar Lahadin da ta gabata ya tabbatar da mutuwar mutane uku a harin da ‘yan bindigar suka kai wadanda rahotanni suka ce sun afkawa al’ummomin kan babura kusan 30.

Basaraken gargajiya na Angwar Fada da ke unguwar Rubu wanda yana daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a harin na ranar Lahadi, Elisha Mari, ya bayyana wa manema labarai a wannan Litinin din cewa, wadanda suka yi garkuwa da su sun sako shi ne don ya fada masu a je a nemo N100m domin a sako sauran da ake tsare da su, inji majiyar Popular News Hausa ta Sunnews.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *