Yakin Neman Zaɓe: Ba Zamu Cutar Da Kowa Ba. Cewar Tsohon Gwamnan ari Abubakar
Daga Hussaini Ibrahim
Tsohon Gwamna Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari kuma shugaban babban kwamitin kamfen na yakin cin nasara zaɓen shekara ta 2023, ya tabbatar da cewa, ba zasu cutama kowa ba a lokacin gudanar da Kamfen na samun nasara zaɓen yan takarar na jami’yyar APC a zaɓe mai zuwa.
Abdul’aziz Yari ya yi wannan jawabi ne wajan ƙaddamar da shugabannin sasa na Yakin zaɓe a sakatariyar Bala Yakubu da ke Gusau.
Yari ya bayyana cewa, sun samar da ƙananan kwamitocin ne dan su faɗada wajan ganin sun samu nasara zaɓe mai zuwa.kuma waɗannan kwamitocin sun haɗa da wayar da kan al’umma, tuntuɓa da tsaro da wasanni da labarai da zirga-zirga da dai sauran su.
Kuma waɗannan kwamitocin ya su fara aiki ne anan take kuma suna ƙarƙashin jagorancin Babban Kwamitin waɗanda a cikin su a kai tsafin gwamnoni da mataimakan su da Sanatoci da Minstoci da dai sauran su.
Tshon gwamna Abdulaziz Yari ya yi kiira ga shugabanin kwamitocin da suji tsoran Allah wajan tafiyar da ayyukan su dan samun nasara a yakin neman zaɓen da suke tunkara.
