September 19, 2026

Ina nan Cikin Jami’yyar APC Kuma Ba Zan Barta Ba. Cewar Shitu Maslaha

0

Tsohon shugaban jam’iyyar APC kuma sakataren jam’iyyar na jihar Katsina Malam Shitu Maslaha ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗa cewa ya koma jam’iyyar PDP.

Kamar yadda ya shaidawa Popular News Hausa cewa yana nan cikin jam’iyyar APC kuma babu abinda zai sa ya barta saboda haka mutane su yi watsi da wancan maganar da ake yaɗa

“Kasan mutane ba zaka iya hana su yin abinda suke son yi ba, amma dai gaskiya magana shi ne , bani da wani tunani na barin jami’yyar APC koma me zai faru.” Inji shi.

Tunda safiyar yau Litinin aka wayi gari da labarin cewa Malam Shitu Maslaha ya bar jami’yyar APC ya koma jam’iyyar PDP, a kafafen yada labarai na zamani,sai dai kuma masu yaɗa irin wancan jita-jitar ba su ƙarin haske akan yaushe ya bar jami’yyar APC ba.

Shitu Maslaha dai na ɗaya daga cikin manyan aminan tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Inuwa da ya bar jami’yyar APC zuwa jami’yyar PDP a kwanakin baya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *