September 17, 2026

Yadda Wani Baturen ‘Yan Sanda Ya Biyawa Wani Saurayi Sadakin Dubu 20 Ga Buduwar A Kaduna

0

Daga Hussaini Yero

Masu iya magana na cewa,na Allah ba ya karewa, musamman ba a cika yiwa ‘Yan Sanda zaton alhairi ba ,sai gashi DPO na Millonia City Kaduna ,Lawal Abdullah ya biya Sadakin Saurayin da aka kai kararsa wajan shi dan ya zaga biyan sadakin dubu Ashirin da aka sa masa anan take DPO Lawal Abdullah ya biya wa Saurayin Aliyu Sadakin dubu hamsin da uku.

Masarautar Dan Bushiya da ke cikin Kaduna ne ta kai karar Saurarayin ga DPO dan yayi amfani da karfin Damaransa wajan raba Aliyu da Buduwarsa Marya wace aka sa masa Sadakin Dubu Ashin ya gaza biya wata da watanni .

kuma Saurayin ya ki rabuwa da Buduwar ta sa shine Sarkin Dan Bushiya da ke jagorantar hidimar ya kai kara Aliyu wajan DPO dan ya rabasu da ita ,sai gashi anan take DPO Lawal Abdullah ya zare kudin har dubu hamsin da uku kamar yadda shri’a ta ce a biya wa Saurayin Sandaki aka daura auren anan take.

Sakataren Sarki Umar Yakubu ya jinjinwa DPO Lawal Abdullah abisa kokarin da yayi na ceto Maryarm daga halin da take ciki dan marainiyace shi Kuma Aliyu Iyayan sa basu da karfin yi masa aure.

Sakataren Sarki ya bayyana cewa,ya kwashe sheru 40 na Sakataren Sarki bai taba ganin ma’aikacin Damaraba mai tausai irin DPO Lawal Abdullah ba.dan su abunda mu kayi tsamani shine Aliyu ya gamu da hukunci mai tsauri dan ya rabu da Maryam ta samu wani ta aura sai gashi reshe ya juye da mujiya Maryam ta zama matar sa gidan ‘Yan Sanda.

Akan haka ne Umar Yakubu yayi kara ga hukumar Rundudar’Yan Sanda da su karawa DPO Lawal Abdullah mukami da lanbar yabo wajan sasanta al’umma dan samun cikaken zaman lafiya .

Sakataren yayi kira ga ‘Yan Sanda da suyi koyi da DPO Lawal Abdullah wajan aiki na gari da sulhunta Jama’a ba tare da anje kotuba .

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *