Ku Zo Mu Yi Aiki Tare Domin Cigaban Jihar Katsina: Kiran Hon. Gwajo-Gwajo Ga ‘Yan Adawa.
Mai baiwa gwamnan jihar Katsina shawara akan harkokin siyasa Hon. Yau Umar Gwajo-Gwajo ya yi kira ga ‘yan adawa da su zo a yi gwamnati domin cigaban al’ummar jihar Katsina baki ɗaya.
Hon. Ya’u Gwajo-Gwajo ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai jin kaɗan bayan shigar sabon ofis na mai baiwa gwamna shawara akan harkokin siyasa.
Tsohon Kakakin Majalisar dokokin ya ce in dai da gaske adawa ake yi, to yana kira da babbar murya da su zo a haɗa kai a ciyar da jihar gaba domin duk abinda ake yi ana domin talaka.
Hon. Gwajo-Gwajo ya ce suna shirye da jin soka mai ma’ana domin a cewar sa soka ba laifi ba ce, idan har zata sa ayi gyara wanda zai amfani al’umma baƙi ɗaya.
“Muna son ɗan adawa ya zo ya faɗi abinda yake ganin ba daidai bane, muna san haka, domin shi duk wanda ya ce gyara kayanka ai baya zama sauke mu raba” inji shi.
A cewar Hon. Yau Umar Gwajo-Gwajo abinda ba daidai ba shi ne, a kawo abu da babu shi, amma don gwamnati ta ce zata yi wani abu ɗan adawa ya ce ba daidai bane, za a tsaya a duba wannan abu a gani domin samun maslaha.
‘Yan adawa muna maraba da ku, muna gayyatar ku, ku zo a yi wannan gwamnati da ku, domin ta haka ne jihar Katsina zata kai wani matsayi da ba a tunani’ inji Gwajo-Gwajo.
Haka kuma ya yi kira ga ‘yan jarida da su bada ta su gudunmawa wajan ganin wannan gwamnati ta Malam Dikko Raɗɗa ta yi nasara, inda ya ce ‘yan jarida suna muhimmiyar rawar da za su taka wajan kawo gyara a tsarin dimokuraɗiyya.
Ya yi kira ga ‘yan jaridar da su cigaba da aikin su ta hanyar tuntuɓar gwamnati akan abinda ya shafe ta kai tsaye, inda ya yi alkawarin cewa kofa a buɗe take akan duk wani ƙarin haske daga ɓangaren gwamnati.
Kazalika ya bada tabbacin cewa wannan ofis ɗin nashi, a shirye yake wajan ganin ya yi aiki da kowane ɓangare tunda ofis ne na siyasa, a cewar sa ofis ɗin yana da alaƙa da kowane ɓangare na gwamnatin jihar Katsina.
Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo ya jaddada kudirin wannan gwamnati ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa da cewa tana da shirye-shirye da take da su akan harkar noma da ilimin da kasuwanci da samarwa da matasa aikin yi.
Daga ƙarshe ya bada tabbacin cewa wannan gwamnati ce da za a yi saman faifai inda ta ce suna maraba da shawarwari domin samun nasarar su ita ce nasarar kowa da kowa.
