Wata Ƙungiyar Tayi Allah Wadai Da Labarin Karin Kudin Wutar Lantarki A Katsina.
An bayyana ƙarin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta sanar kwanan nan a matsayin abin Allah wadai da rashin tausai.
Shugaban ƙungiyar cigaban Badumasia Alhaji Sani Bawa Dutsinma ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Katsina.
Ya bayyana cewa, ƙarin kuɗin wutar a daidai wannan lokaci bai dace ba, saboda har yanzu yan Najeriya basu murmure ba sakamakon cire tallafin mai da gwamnati mai yanzu ta yi.
Kamar yadda ya ce, yakamata gwamnati mai ci yanzu ta maida hankali wajen gyara yanayin tattalin arziki da ta gada daga gwamnatin da ta gabata.
Ya ce abin takaici ne gwamnati mai ci yanzu ta cigaba da aiwatar da tsare-tsaren da zasu jefa yanayin tattalin arziki ciki wani hali da kuma cire tallafin ɓangarori da dama, kuma a halin yanzu a ce za a ƙara cire tallafin kuɗin wutar lantarki.
Don haka, Alhaji Sani Bawa Dutsinma ya yi kira ga gwamnati mai ci yanzu ta gaggauta sakr duba matakin da ta ɗauka akan ƙarin kuɗin wutar lantarkin da ta sanar kwanan nan.
