November 19, 2026

Wata Cibiya Ta Karrama Gwamnan Jiha Katsina Da Lambar Yabo.

0

Wata cibiya mai suna Michael Imoudu National Institute for Labour Studies ta karrama gwamnan jihar Katsina ABM da lambar zama abokin hudda ga kungiyoyin ƙwadago.

Mai ba gwamnan jihar Katsina shawara akan harkokin ƙwadago Tanimu Lawal Saulawa ne ya fadi hakan a lokacin kaddamar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin kungiyar yan fansho ta Najeriya reshen jihar Katsina, wanda ya gudana a dakin taro na Multipurpose.

Mai ba gwamnan shawara wanda ya samu wakilcin daraktan mulki Hassan Abdulkadir, ya ce gwamna Masari na biyan kuɗin albashi dana fansho cikin lokaci.

Ya dai taya sabbin zaɓaɓɓun shugabannin kungiyar murna, tare da yin kira su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da aka dora masu.

Shugaban kungiyar yan fansho na Najeriya reshen arewa maso yamma Muhammad Dankande ya yaba ma yan fanshon bisa nuna halin dattako a lokacin zaben, tare da yaba ma shugaban kungiyar mai barin gado bisa tabbatar masu da matsugunni na dindindin.

A jawabinshi na bankwana, tashon shugaban kungiyar mai barin gado Mahabubu Balarabe Daura ya gode ma yan fanshon bisa goyan bayan da suka ba shi a lokacin da yake shugabancin kungiyar.

Jami’in hukumar zaɓe na ƙasa Ahmad Gazali shi ne ya gabatar da takardun shaida, tare da bada rantsuwar kama aiki ga sabbin shugabannin kungiyar.

A saƙon shi na godiya, sabon shugaban kungiyar Usman Muhammad Yar’adua ya yaba, tare da neman goyan bayan ƴaƴan kungiyar a lokacin shugabancin shi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *