November 18, 2026

Kotu Ta Yanke Ma Mutane 4 Hukuncin Rataya a Jihar Osun.

0

Wata babbar kotun Osun da ke zamanta a Osogbo, a wannan Litinin din ta yanke ma wasu mutane hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da laifin kisan kai da sauran laifuka masu alaka da haka.

Wadanda aka yanke wa hukuncin su hudu da suka haɗa da Olabisi Bashiru mai shekaru 50, Kayode Sunday mai shekaru 27, Rashidi Waidi mai shekaru 35, da kuma Hameed Rafiu mai shekaru 33.

Sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da aikata.

Alkalin kotun mai shari’a S. Falola, ya yanke wa mutanen hudu hukuncin kisa saboda girman laifin da suka aikata.

Lauyan jihar, Mr. Dele Akintayo, ya shaida wa kotun cewa wadanda aka yanke wa hukuncin sun aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Nuwamba na 2018 da misalin karfe 2:00 na rana a unguwar Moboreja, Ikirun, Osun.

” Wadanda aka yanke wa hukuncin dauke da muggan makamai sun tsallaka gidan wani mutum mai suna Victor Akinbile suka shiga dakin da yake barci da karfin tsiya.

” Sun bukaci Akinbile ya ba su Naira miliyan 10, amma ya ba su Naira miliyan 3 ta hanyar tura masu a asusu, tare da yin barazanar barazanar kashe shi.

“Mutanen da aka yanke ma hukuncin daga baya sun yi garkuwa da Akinbile, suka sanya shi cikin but din motarshi sanfarin Toyota Camry, tare da kai shi wani sansani mai suna Dominion, akan hanyar Iragbiji, bisa hanyar Ikirun/Osogbo, sannan suka cinnama motar wuta yana ciki, abinda ya jaza mutuwarshi (Akinbile).”

Lauyan mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da dokar fashi da makami ta 2004, wanda aka zartar a karkashin kundin laifuffuka, Cap 34, Volume 2, Laws na 2002.

Lauyan wadanda aka yankewa hukuncin, Mr. S. Ajibade da Mr. Adedayo Adedeji, sun roki kotun da ta yi rahama wajen yanke masu laifin hukunci, a cewar majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *