Wani Titi Ya Zama Abun Damuwa A Dutsinma, Katsina.
Titin Gidan Nagari zuwa gidan man Shema da ke Dutsinma mai tsawon kilomita 1.5 da ɗan majalisar dokokin mai wakiltar Dutsinma/Kurfi ya gina, ya zama babban abun damuwa ga mutanen da ke rayuwa a yankin.
Aikin wanda aka yi cikin hanzari ya bar baya da ƙura domin babu magudanan ruwa, babu kwalbati, sannan ba a gyara ma mutane fayib ɗin ruwansu ba.
Titin baya biyuwa cikin daɗi, abinda ya tilasta ma al’ummomin Kadangaru da kewayenta yin kira ga ɗan majalisar ya sake maido ɗan kwangilar wurin aikin.
Shugaban ƙungiyar cigaban Kadangaru Shehu Harisu ya yi wannan kiran yayinda ya ke magana da wakilinmu na shiyar Dutsinma.
Shugaban da ya samu wakilcin sakataren ƙungiyar Kabir Sule, yayi nuni da cewa al’ummomin da ke wurin na jigatuwa dalilin wannan matsalolin da aka ambata a sama.
Saboda haka, Shehu Harisu ya faɗa ma al’ummomin cewa, ƙungiyar ta miƙa takardar koke ga shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Dutsinma.
Shima da yake magana, hadimin ɗan majalisar dokokin Mannir Gambo Dutsinma ya faɗa ma al’ummomin cewa, ɗan majalisar ya bada tabbacin sanya baki da kuma gyara matsalolin.
