September 18, 2026

Al’ummar Mahuta Sun Bayyana jindaɗi Ga Agile Bisa Gyara Masu Makarantar Sikandiren.

0

 

Iyaye, malamai da ɗaliban na makarantar sikandiren jeka-dawo ta gwamnati da ke Mahuta cikin ƙaramar hukumar Dandume sun bayyana jindaɗi bisa tallafin bunƙasa ilimi da shiri “Agile” ya ba makarantar domin bunƙasa ayyukanta.

Shugaban makarantar Muhammad Abdulsalam da shugaban kwamitin tabbatar da ingantaccen ilimi na makarantar (SBMC) Magaji Yusuf suka bayyana hakan a lokacin wata zantawa da manema labarai a farfajiyar makarantar.

Sun yi wannan yabon ne akan aikin da shirin Agile ya gudana a makarantar karo na biyu.

Wata ziyara da aka kai makarantar ta nuna cewa, an ba makarantar Naira miliyan 8 domin gyara azuzuwa, masaukin matasa masu yima ƙasa hidima da kuma samar da kujeru da tebura.

Kamar yadda shugaban makarantar Mohammed Abdulsalam ya bayyana, an bada gyaran azuzuwa 9 masu rukuni 3, ƙari ga aikin gina sabbin azuzuwa 2.

Shugaban makarantar ya ce a baya makarantar ta amfana da aikin Agile a kashin farko, kuma ya bunƙasa yanayin koyo da koyarwa matuƙa a makarantar.

Mohammed Abdulsalam ya ce akwai ɗakin gwaje-gwaje mai ɓangarori daban daban da sabbin ban-ɗakuna 3 da ake ginawa.

A lokacin ziyarar, an fahimci cewa aikin ya kai kaso kimanin 70 cikin 100 na kammaluwa.

Injiniyan da ke duba aikin Abdulmumin Shehu ya bayyana gamsuwa da irin aikin da aka yi da kuma kayan aikin da aka yi amfani da su a wajen aikin.

Shugaban kwamitin shugaban kwamitin tabbatar da ingantaccen ilimi na makarantar Magaji Yusuf ya ce an kashe kuɗin da aka samar bisa ka’idojin da shirin Agile ya gindaya.

Magaji ya ce suna gudanar da aikin tare da sauran abokan aiki, da kuma membobin kwamitin aiwatar da aikin kafin gudanar da wani abu.

Ya gode ma Dikko Umaru Radda bisa ƙoƙarin bunƙasa ɓangaren ilimi, masamman ma daga tushe.

Mataimakin shugaban makarantar Malam Sani Shehu ya bayyana gamsuwa akan ƙwararen matakan da shirin Agile ya ɗauka akan yadda ya kamata a kashe kuɗin aikin.

Ya bada tabbacin yin amfani da kuɗin da aka ba hukumar makarantar yadda ya kamata.

Ya yi kira ga ma’aikatar ilimi ta jiha ta kewaye makarantar domin magance shigowar mutane da dabbobi ba kan gado a cikin makarantar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *