Uwar Jam’iyyar APC Ta Kasa Na Shirin Rantsar Da Dan Zago a Matsayin Shugaban APC na Kano a Yau
A yau Alhamis jam’iyyar APC za ta rantsar da shugabannin jam’iyyar na jihohi dake biyayya ga gwamnonin jam’iyyar sai dai rahotanni sun bayyana cewa za a rantsar da tsagin dake adawa da Ganduje a jihar Kano.
Jihohi da dama sun rabu gida biyu sakamakon rikicin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan zaben shugabanninta a matakin jihohi.
Jaridar Punch ta rawaito cewa, shugabannin jam’iyyar daga jihohi 30 sun isa birnin tarayya Abuja domin bikin kaddamarwa.
Rahotanni sun bayyana cewa an jibge jami’an tsaro a shelkwatar jam’iyyar ta APC.
