Masu Neman Takarar Karamar Hukuma A Katsina sun Kai 150 –Sakataren Jam’iyyar APC
Sama da masu neman takarar Shugabancin Kananan Hukumomi su 150 a karkashin Jam’iyyar APC ne suka sayi Tikitin tsayawa takara a Jihar Katsina.
Sakataren Mulki na Jam’iyyar Alhaji Sani Aliyu ne ya tabbatar da hakan a lokacinda yake zantawa da wakilin Jaridar The Fact 24.
Kamar yadda ya bayyana,sama da mutane 1000 ne suka sayi tikitin neman takarar Kansila a fadin Kananan Hukumomi 34 da ke Jihar.
A cewarshi,a halinda ake ciki Jam’iyyar a matakin Jiha tana a matakin Karbar takardun yan takara da suke neman Shugabancin Kananan Hukumomi.
A dayan bangaren kuma,yan takarar Kansila suna maida takardun nasu a Ofishin Jam”iyyar na Kananan Hukumominsu.
Sakataren Harkokin Mulkin ya yabawa Gwamna Aminu Bello Masari akan yadda ya nuna halin dattaku wurin sha’aninda ya jibanci fitowa da yan takara.
Alhaji Sani Aliyu yace Gwamnan baya da ra’ayi ko daya akan wani dan takara,wanda hakan ya nuna shi adali ne.
Daga nan sai ya Jaddada yakinin cewar APC ce zata lashe zaben in Allah ya yarda.
