September 18, 2026

Tsakanina Da ‘Yan Bindiga Sai Kisa Idan Na Zama Sanatan Shiyyar Funtua – Dandutse

0

Mai neman tikitin takarar Sanatan shiyyar Funtua a jihar Katsina Mukhtar Dandutse, ya ja kunnen ‘yan bindiga da ke ta’addanci a shiyyar dama sauran sassan jihar Katsina da su rungumi sulhu ko kuwa jikinsu ya faɗa musu.

Mukhtar Dandutse wanda yanzu haka shi ne ɗan majalisar wakilan Najeriya da ke wakiltar ƙananan hukumomin Funtua da Dandume, ya yi wannan jan kunnen ne a lokacin ƙaddamar da neman takarar sa a shiyyar.

Ya ja kunnen cewa, muddin aka zaɓe shi a matsayin Sanata, to kuwa waɗannan ‘yan ta’addar ba su da sauran shan ruwa kuma kofar tuba ta rufe a lokacin, tsakaninsa da su sai kisa.

Mukhtar Dandutse ya jaddada cewa mutane na buƙatar su zauna lafiya domin su cigaba da hulɗoɗinnsu na yau da kullum har tattalin arzikin su ya farfaɗo.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *