November 17, 2026

2023: Ɗandutse Ya Shirya Kawar Da Sanata Bello Mandiya

0

Kwanaki kalilan gabanin zaɓen fitar da gwanin jam’iyyar APC, ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Funtua da Ɗandume a majalisar wakilan Najeriya Mukhtar Dandutse ya shirya tsaf domin karbar kujerar Sanatan shiyyar Funtua daga hannun Bello Mandiya a babban zaɓe mai kamawa.

Mukhtar Dandutse na magana ne a babban gangamin da ya shirya a shiyyar Funtua domin bayyana aniyarsa ta neman tikitin takarar Sanatan shiyyar.

Dandutse ya yi nuni da cewa yana da gogewar da ta kamata da zai iya wakiltar shiyyar ta Funtua, inda ya lissafo wasu daga cikin nasarorin da ya samu a kasancewarsa shugaban ƙaramar hukumar Funtua da kasancewar sa ɗan majalisar wakilai har karo uku a majalisar dokokin Najeriya.

“Cikin waɗannan shekarun, na samu damar gina makarantu, asibitoci da samar da ayyukan yi ga matasa da ba da tallafin sana’o’in hannu ga mata da matasa a yankin. Na yi alkawarin ci gaba da waɗannan ayyukan muddin aka zaɓe ni a matsayin Sanata”, inji Dandutse.

Ya yi nuni da cewa yankunan shiyyar Funtua da ke fama da matsalolin tsaro nan da can, na da buƙatar jajirtaccen mutum mai gogewa da kwarewa domin shawo kan matsalar cikin kankanin lokaci.

Dan majalisar wakilan ya buƙaci ‘ya’yan jam’iyyar APC da shugabannin ta da wakilai wato ‘delegates’ da su bashi goyon baya ya samu nasarar zaɓen domin shiyyar Funtua da ɗaukacin jihar Katsina ta cigaba da cin moriya.

A nasa tsokaci, shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Funtua, Ibrahim Ɗanjuma Malumfashi, ya ce ba su day wani dan takarar da ya wuce Mukhtar Dandutse a kujerar Sanatan shiyyar.

Ya yi nuni da cewa Dandutse mutum ne mai gaskiya, juriya, hakuri da riƙon amana da yake da son al’ummar sa a rai.

Shi ma da yake jawabi, jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar APC a jihar Katsina Shamsu Sule ya yi takaicin cewa tun da Sanata Abu Ibrahim ya sauka daga muƙamin Sanata a shiyyar Funtua, shiyyar ta rasa gatan da take samu. Ya ba da tabbacin cewa Mukhtar Dandutse zai dawo da martaba da kimar shiyyar Funtua tare da tabbatar da an tafi da kowa da kowa a cikin tafiyar.

Dubun dubatar jama’a dai ne suka halarci taron gangamin da kwamitin yakin neman zaɓen Dandutse ya shirya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *