September 17, 2026

Tawagar Atiku Ta Zo Katsina Neman Goyan Baya Ko Dinke Barakar ‘Ya “yan Jam’iyyar PDP?

0

Daga Wakilinmu

Rahotanni sun tabbatar da zuwa wata tagwa mai karfin gaske wanda dan kasuwa kuma dan siyasa shugaban kamfanin Daar Communication Chief Reymond Dakpesi.

wanda kuma ya zo Katsina domin ganawa da shuwagabanin ita jam’iyyar PDO na Katsina.

Tun da farko dai Chief Reymond Dakpesi. ya ce wannan tawaga ta zo Katsina ne akan hanyar ta ta zagaye Najeriya domin gudnar da tuntuba dangane da batun tayawar takarar tsohon mataimakin shugaban KAsa Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa)

Masu sharhin akan al’amuran siyasa tuni suka fara bada fassara game da wannan ziyara ta…. Inda ita wannan ziyara ga fara hada kan ‘ya ‘yan jam’iyyar a wuri guda domin gudanar da taron abinda aka dade ba a gani ba.

Wanda dai shi ne taro irin na farko tun bayan hukuncin kotu daukaka kara game da rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar a jihar Katsina tun bayan zaban shuwagabanin da aka yi matakin runfa da kananan hukumo da kuma jiha, wanda ya bar baya da kura.

Sai dau kuma wasu na ganin tunda siyasa kasuwar bukata ce, babu mamakin ganin fuskokin da mutane da suka koma gefe suna fadin da shugabaicn jam’iyyar amma yanzu ga Atiku nan ya turo dan sako saboda haka dole ne kowa ya zo ya ji ya kuma ga abinda zai faru.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *