Ƙungiyar K34 Na Kiran Dakta Mustapha Inuwa Da Ya Tsaya Takarar Gwamna 2023.
Wata Ƙungiya mai zaman kanta tayi kiran Dr Mustapha Muhd Inuwa Sakataren gwamnatin Jahar Katsina daya fito takarar gwamnan Katsina a 2023 domin karasa ayyukan da mai girma gwamna Masari ya fara.
Wannan kiran yana fitowa ta bakin shugaban Ƙungiyar Alh Abubakar Tsanni a wata zantawa da sukayi da jaridar Katsina post a ranar Lahadi nan, inda ya bayyana cewa zasu tsaya-tsayin daka domin samun nagartaccen mutum wanda zai karasa ayyukan da gwamnatin ta fara.
“Ya rike Sakataren gwamnati har sau 3 sannan yayi ciyaman na jam’iyya gamida kwashinan ilimi ba’a taba samun sa da wani almubazzaranci ba” inji Dr Tsanni.
Tsanni ya kara da bayyana Cewa Ƙungiyar su bazata bari A rasa irin wannan haziki gwamnatin Jahar ba.
