September 19, 2026

Tasirin Sauyin Yanayi: Najeriya Ce Ta Biyu A Cikin Kasashe 163 – Rahoto.

0

Rahoton Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da aka fitar a ranar Juma’a ya bayyana Najeriya a matsayin mafi girma cikin hadarin illar sauyin yanayi, wadda ke ta biyu a cikin kasashe 163.

Kamar yadda asusun UNICEF ɗin ya bayyana, “Yaran da ke cikin kasashen da ke da matukar haɗarin sauyin yanayin suna fuskantar matsalolin muhalli saboda rashin isassun ayyuka masu mahimmanci ga rayuwarsu, kamar su ruwan sha, tsabta, kiwon lafiya da kuma ilimi. ”

Rahoton ya kuma yi nuni da cewa sama da yara miliyan daya da rabi ne ke cikin hadari sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa wasu sassan Najeriya.

“Fiye da mutane miliyan 2.5 wanda kaso 60 cikin 100 na su yara ne kanana na bukatar ayyukan jin kai a Najeriya, kuma suna fuskantar barazanar kamuwa da cututtukan ruwa, matsalar yunwa, bannar ambaliyar ruwa mafi muni a cikin shekaru goma da suka gabata.

“Ambaliyar da ta shafi jihohi 34 cikin 36 na kasar nan, ta raba mutane miliyan 1.3 da muhallansu, yayin da sama da mutane 600 suka rasa rayukansu, sama da gidaje 200,000 sun lalace.”

“Cututtukan amai da gudawa, cututtukan da ake dauka cikin ruwa, cututtukan lumfashi da kuma na fata na ƙaruwa.”

“A jihohin Borno da Adamawa da Yobe da ke arewa maso gabas kadai, an samu rahoton bullar cutar kwalara 7,485 da kuma mutuwar mutane 319 a ranar 12 ga watan Oktoba, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *