September 18, 2026

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Oborevwori A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar PDP A jihar Delta.

0

Kotun Koli ta tabbatar da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, Sherrif Oborevwori, a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna mai zuwa a jihar Delta a wannan Juma’ar, inji majiyar Popular News Hausa ta Vanguard.

Kotun kolin, a wani mataki na bai daya da tawagar alkalanta mai mutune biyar karkashin jagorancin mai shari’a Amina Augie, ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar, Olorogun David Edevbie ya shigar kan Oborevwori.

Edevbie ya daukaka kara, inda ya yi zargin cewa Oborevwori ya mikawa jam’iyyar PDP takardun jabu, domin neman cancantar tsayawa takara a zaben da aka gabatar a ranar 11 ga Maris, 2023.

Ya ce Oborevwori ya mallaki takarar rantsuwar kotu mai cewa an haife shi a shekarar 1963, saidai ya bada sakamakon WAEC na wani mai ɗauke da shekarar 1979.

Mai shigar da karar ya dage cewa duk takardun da Oborevwori ya mika wa jam’iyyarsa, na goyon bayan takardunshi na tsayawa takara, basu yi daidai da sunansa ba da shekarun haihuwa.

Bayan haka, Edevbie ya kyas din ya samar da dama ta masamman ga Kotun Koli ta sashe na 29(5) na dokar zaɓe 2022.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *