Taron Baje-Kolin Finafinan Afirika ‘KILAF Award 2023’ Shirye-shirye Sun Kankama
DAGA MUKHTAR YAKUBU
A daidai lokacin da a ke cigaba da shirye-shiryen bikin Baje kolin finafinai na Afirka ‘wato “African Indigenous Language Filims’. Mai taken ‘Kano Indigenous Languages Of Africa Film Market & Festival’ KILAF AWARD, da aka saba shiryawa duk shekara a garin Kano.
A yanzu haka dai an kai ga matakin tantance finafinan da su ka shiga gasar domin fitar da waɗanda za su kai matakin cancanta da kuma waɗanda ba su kai ba.
Alkalan gasar dai su bakwai ne da su ka haɗa da Victor Okhoir,da Emmanuel Emascalu da Charlas Okwuowulu da Falakemi Ogungbe, Izu Ojukwu, Charity Torut, da kuma Alwine Allen.
A wannan shekarar dai an samu karin finafinai da su ka shiga gasar fiye da shekarun da su ka gabata, inda aka samu finafinai guda 46 da su ka shiga daga ƙasashen duniya daban-daban da su ka haɗa da Nijeriya da Masar da Afirka ta Kudu da Tunusiya da Ghana.
Sauran sun haɗa da Tanzaniya da Aljeriya da Ajantina da Benin da Botswana da Kamaru Kodebuwa da Jamus da Gini Bissau da Kenya Malawi da Mozanbiq da Potugal da Amurika da kuma Zumbabuwe.
Kamar yadda Daraktan gudanarwa na bikin KILAF AWARD 2023 Nasir B. Muhammad ya yi mana ƙarin bayani dangane da taron na bana, ya ce “A wannan shekarar an samu sauye sauye, saboda ci gaban zamani da a ke samu, don haka tantancewar ma ta kafar sadarwa ta zamani za a yi ta.
Saboda a cewar sa Alkalan sun fito ne daga sassa daban-daban na duniya don haka sai aka tsara gudanar da tantance su ta internet, amma a mataki na ƙarshe za a haɗu a waje guda don fita da sakamakon gasar”.
Shin ko ya wannan taro na bana zai kasance? sai ya kada baki da cewa
“To kamar yadda muka saba a baya, a wannan ma dai akwai babban taro da muke yi a BUK wanda za a karanta maƙaloli wannan taron yana da muhimmanci a cikin tsarin shirye shiryen mu.
Sannan akwai babban aji na koyar da harkar fim wanda shi ma na bana ya zo da wani tsari na daban domin mun samar da kwararrun masana a kan harkar fim da za su koyar.
Ya cigaba da cewa ‘To ka ga duk wanda yake jin kan sa shi mai sana’ar fim ne, kamata ya yi ya zo ba sai an gayyace shi ba.’ Sannan akwai abincin Afirka da ake gudanarwa a taron, don haka muna gayyatar duk wanda yake ganin ya kware a fagen tsara abinci na Afirka.
Nasir B Muhammad wanda ya ce akwai finafinai da za a nuna su a sinima kuma waɗanda suka shirya finafinan za a gan su a wajen da duk wanda yake da wata tambaya ya yi musu, saboda haka ni ina ganin wannan wani abu ne kamar an haɗa karfi da karfe, domin a ga mun kai wani mataki na gaba.
Haka kuma yana mai cewa akwai cin abinci na musamman da za a shirya wa baki sai kuma ranar Award da za a gayyato baki daga ko’ina domin su halarci wajen, don haka nake ganin duk wani mutum da yake da kishin ci gaban harkar fim, taron na sa ne ba sai an gayyace shi ba, don shi ma mai gayyata ne, domin dama ce da zai haɗu da mutane kuma ya koyi abubuwa masu damar gaske, kuma dandali ne na shirya mu’amala da kuma kasuwanci tsakanin mu da abokan harkar mu na ƙasashen Afirka.
Don haka muna fatan za a ba mu haɗin kan da ya kamata”.
