Takarar Gwamnan Katsina: Injiniya Nura Khalil Ya Shirya Tsaf Domin Neman Kujerar Gwamna A Zaɓen 2023
Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Katsina kuma jigo a siyasar jihar wato Injiniya Nura Khalil, ya shirya tsaf domin neman Kujerar Gwamnan Jihar ta Katsina a Zaben Shekarar 2023.
Injiniya Nura Khalil zai nemi takarar ne a karkashin Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, da al’ummar Najeriya ke yiwa lakabi da jam’iyyar kafa sabuwar Nigeria.
Tuni dai Injiniya Nura Khalil ya sayi tikitin neman takarar a shalkwatar Jam’iyyar ta Kasa da ke Birnin Tarayya Abuja.
Fitowar Injiniya Nura Khalil domin neman takarar, ya biyo bayan kiraye-kirayen da yake ta samu daga al’umma na kowane bangare na jihar Katsina, lura da nagartar shi da suke gani wurin jagorantar al’ummar Jihar.
Sanin kowa ne cewar Injiniya Nura Khalil, ya sha gwagwarmaya sosai a siyasar jihar Katsina a matakai daban-daban Tun daga shekaru sama da 30 da suka gabata, kuma ya taka gagarumar rawa ta fuskar kawo cigaban harkokin siyasar a jihar Katsina da ma Kasa baki daya.
Injiniya Nura Khalil ya taba zama Dan Takarar Gwamnan Jihar ta Katsina a 2003 a karkashin Jam’iyyar ANPP, inda ya yi takara da Marigayi Shugaban Kasar Najeriya Malam Umaru Musa Yar’adua da sauran yan takara.
Bugu da kari a kakar zabe ta shekarar 2019, Injiniya Nura Khalil ya yi takarar Sanata na Shiyyar Funtua a karkashin Jam’iyyar APC.
Kwararren Injiniya, Alhaji Nura Khalil mutum ne mai tausayin mabukata da tallafa masu, wanda hakan ya bashi damar kafa wata gidauniya ta taimaka wa Marayu da sauran mabukata wato Nura Khalil Foundation, kuma take aiki ka’in da na’in a fadin lungu da sako na Jihar Katsina.
Abinda ya yi saura a nan shine, al’ummar Jihar Katsina su jaraba Injiniya Nura Khalil ta hanyar zaben shi ya jagoranchi jihar Katsina domin bashi sukunin cigaba da aiwatar da ayyukan jin kan al’umma da ya saba gudanarawa.
