September 19, 2026

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Rabawa ‘Yan Banga Kaki 500 Domin Gudanar Da Aiki Cikin Nasara.

0

Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin shugabancin gwamna Aminu Bello Masari ta rabawa ‘yan banga Kaki domin gudanar da aikin su cikin kwanciyar hankali da lumana.

Mai baiwa gwamna shawara akan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina ya bayyana haka a lokacin da yake miƙa kayayyakin ga shugaban ‘yan banga na jihar Katsina a madadin gwamnatin jihar Katsina.

Alhaji Ibrahim ya ƙara da cewa dole a taimakawa ‘yan banga duba da irin kokarin da suke yi tare da jami’an tsaro wajan dakile ta’addanci a jihar Katsina da ke fama da matsalar tsaro tsawon lokaci.

Mai baiwa gwamna shawara ya ce kayayyakin da aka baiwa ‘yan bangar sun haɗa da riga da wanda da takalma da hula da kuma bale domin taimakawa kokarin su na aiki tukuru.

Shima da yake karɓar wannan gudunmawa a madadin kungiyar ‘yan banga shugaban jam’iyyar Salisu Rabo ya bayyana jin daɗin su akan wannan karamci da aka yi masu.

Ya kuma bada tabbacin yin aiki da wannan gudunmawa domin ganin an yi aiki tare da sauran jami’an tsaro domin tunkarar ƙalubalen tsaron da ake fuskanta ba dare ba rana

“A shirye muke wajan haɗa hannu da sauran jami’an tsaro ayi aiki tare a samu nasara, kuma wannan kayan aiki da aka ba mu za su ƙarama mana kwarin gwiwa wajan gudanar da aikin mu” inji shi

Daga ƙarshe mai baiwa gwamna shawara akan harkokin tsaro Ibrahim Katsina ya miƙa kayayyakin a madadin gwamnatin jihar Katsina.

Popular News Hausa

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *