Takarar Gwamna 2023: Mutanen Raɗɗa Sun Sallamawa Mustapha Inuwa
Mai girma sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha Muhammed Inuwa ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Katsina a zaɓen 2023 ya ƙarbi bakuncin wata tawagar matasa daga garin raɗɗa dake ƙaramar hukumar Charanci , a cikin wata ziyara da suka kawo mashi a yau gidanshi dake birnin katsina.
A lokacin da shugaban matasan yake gabatar da jawabi ga mai girma sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha Muhammed Inuwa a cikin ziyarar da suka kawo mashin shugaban ya bayyana cewa sunzo ne domin jaddada goyon bayansu ga tafiya a gudurin tsayawa neman takarar kujerar Gwamnan Jihar Katsina a zaɓen 2023 da al’ummar jihar Katsina suke kiranshi yayi.
Matasan sun kara da kira ga mai girma sakataren Gwamnatin jihar Katsina akan ya taimaka ya amince da ƙiran da al’ummar suke yi mashi domin zama magajin mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masari a shekarar 2023 domin cigaba da kawoma al’ummar Jihar Katsina ayyukan alƙairi na ciagaba a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar APC.
Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha Muhammed Inuwa ya bayyana godiyarshi ga matasan a bisa ziyarar nuna goyon bayan da suka kawo mashi tare da kira a gareshi ya fito neman takarar kujerar Gwamna.
Dr. Mustapha Muhammed Inuwa ya ƙara da bayyanawa matasan cewa a matsayinsu na ƴan siyasa masu kishin al’ummar jihar Katsina saboda ganin an samu cigaba a shirye suke idan lokaci yayi domin fitowa su bada kowace irin gudunmuwace.
Dr. Mustapha Muhammed Inuwa ya ƙara da ƙira ga matasan inda ya bayyana cewa a matsayinku na ƴaƴan Jam’iyyar APC ya kamata ku tashi tsaye wajen tallata irin ayyukan alƙairi da shugabannin wannan Jam’iyya suka yi ma al’umma
A cewarsa hakan zai ƙara sanyawa al’umma su fahimci manufar Jam’iyyar da kuma wanda aka tsaida takara ta kowace irin kujera ce a ƙarƙashinta, harma suyi sha’awar ƙara zaɓenta.
Credit.
Mustapha Rabi’u.
Chairman SGS Social Media Crew.
