‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 17 A wani Sabon Hari Da Suka Kai
Yan bindiga sun kashe akalla mutane 17 a lokacin da suka kai sabon farmaki kan wasu kauyuka da ke kananan hukumomin Wushishi, Lavun da kuma Mashegu a jihar Neja.
Bayanai daga yankunan sun ce, tashin hankalin ya soma ne da tsakar ranar jiya Asabar zuwa akalla 8 na dare, lamarin da ya tilastawa mutane masu. yawan gaske tserewa daga gidajensu.
Wasu mazauna yankunan da suka tsira sun ce ‘yan bindigar haye kan Babura sun rika afka musu ne daya bayan daya, inda suka kaiwa kauyuka fiye da 20 farmaki tare da sace mutane da dama.
A karamar hukumar Lavun, rahotanni sun ce akalla kauyuka 10 ‘yan ta’addan suka afkawa, 6 a karamar hukumar Mashegu, sai kuma wasu karin kauyukan a karamar hukumar Wushishi.
Sai dai har yanzu babu karin bayan ikan wadannan alkaluma daga hukuma.
Daga shafin RFI
