September 16, 2026

Dokar Zabe Ta 2021: Shugaba Buhari Ya Gayyatowa ‘Yan Siyasa Sabuwar Fitina

0

Buhari ya sanya hannu a ƙudirin dokar zaɓe na 2021

A yau Juma’a ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan ƙudirin dokar zaɓe na 2021 da aka yi wa kwaskwarima Kuma.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa an daɗe ana jiran shugaban ya rattaba hannu duk da kiraye-kiraye da a ke ta yi kan ya sanya hannun.

Shugaban ya rattaba hannu kan ƙudirin da misalin ƙarfe 12:25 na rana a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryar biki da ya samu halartar shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da dai sauransu.

Ya ce dokar zaɓen da ya sanya wa hannu ta zo da babbanci gaba domin “zata ba da damar yin zabe cikin gaskiya kuma a bayyane.”

Sai dai Buhari ya bukaci majalisar kasar nan ta sake yin aiki ga dokar don ta haramta wa masu rike da mukaman siyasa shiga takara domin ya dace da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.

Daily Nigerian Hausa

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *