Ta Kowane Ɓangare Yakubu Lado Ya fi Dikko Raɗɗa -Majigiri
Daga Mamman Faruk, Katsina
Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP wanda ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan jihar Katsina Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya ce Sanata Yakubu Lado ya yi wa Dikko Umar Radda nisa ta kowanne bangare.
Hon. Majigiri ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina.
Shugaban jam’iyyar PDP ya ce ɗan takarar su na gwamna Sanata Yakubu Lado ba tsaran Dikko bane na jam’iyyar APC saboda haka suke da fatan lashe zaɓe ba tare da ɓata lokaci ba.
“Ba za a taɓa haɗa Dikko da Lado ba ta kowane ɓangare saboda Lado ɗan siyasa ne tunda daga matakin farko, ya yi Kansila, ya yi Ciyaman ya yi ɗan majalisar tarayya ya yi Sanata duk da cewa Dikko shi ma ya yi ciyaman amma Lado ba tsaransa ba ne” inji shi
Ya ƙara da cewa Lado ya fi Dikko kwarewa a duk bangarori musamman na mulki da sha’anin jama’a, ya ce wannan ke ƙara ba su damar cewa lallai a zaɓen 2023 APC shareta kawai za su kowa ya yi huta.
Da ya yake kira bayani akan irin ƙwarin gwiwar da suke da shi na lashe zaɓen 2023 Majigiri ya ce ‘ yan Najeriya sun yi kuskure wajan zaɓar
APC amma yanzu yana da wahala su sake yin irin wancan kuskuran saboda sun ji a jikinsu.
“Idan ka duba yanayi da tsarin da jam’iyyar PDP ta fitar da ‘yan takara tunda daga ‘yan majalisar jiha zuwa shugaban ƙasa kawai ya isa ya gaya maka abinda zai faru idan aka zo zaɓe.” Inji Majigiri
A cewar Majigiri kasa fitar da mataimakin shugaban ƙasa da jam’iyyar ta yi cikin tsari ya nuna jam’iyyar APC na neman abokin mutuwa Kuma ita kaɗai zata mutum.
Hon. Majigiri ya yi ƙarin haske dangane da batun kowarsa shugaban jam’iyyar PDP bayan ya faɗi zaɓen fidda, inda ya ce a tsarin jam’iyyar su ta PDP ya ba su damar su yi kowace irin takara ba tare da sun ajiye muƙamin su ba, saboda hakan bayan ya faɗi takara ya koma kujerar shugabancin jam’iyyar PDP ta jihar Katsina.
Ya ce kamar shi na batun lokacin da zai yi takara zai miƙa tafiyar da sha’anin jam’iyyar PDP a hannun ma’taimakin sa Alhaji Salisu Uli, yanzu kuma ya dawo zai cigaba daga inda ya tsaya.
Majigiri ya ƙara da cewa su a jam’iyyar su ta PDP sun yarda duk wanda bai samu nasara ba zo ayi aiki tare kuma babu ya ja da haka, ya ƙara cewa yanzu haka suna cigaba da shirye-shiryen jawo kowane ɗan jam’iyya domin tunkarar zaɓe mai zuwa na. 2023.
“Mun yi sa’ar samun Atiku Abubakar a matsayin ɗan shugaban ƙasa da Efeayi Okowa a matsayin mataimakin sa na jam’iyyar PDP haka kuma
