Shugaban Jam’iyar AA Na Jihar Katsina Ya Nemi Taimakon Al’umma Gabanin Zaben Dake Tafe.
Shugaban jam’iyar Action Alliance wato AA na jihar Katsina ya bukaci magoya bayan jami’yar da sauran al’umma su taimaka ma jam’iyar a lokacin babban zaben dake tafe.
Bawale Sani Bakori ya yi wannan kiran ne a lokacin taron shirye shiryen fara gangamin yaƙin neman zaben jam’iyar a shiyyar Funtua.
Ya ce jam’iyar da ta tsaida Garba Sani Dankane a matsayin dan takarar ta na gwamna, za ta kawo sauye sauyen da ake bukata a jihar Katsina.
Shugaban jam’iyar ya ce idan aka zabe su, to jami’yar zata maida hankali wajen ganin ta samar da abubuwan more rayuwa kyauta ga al’ummomin jihar ta Katsina, wanda kuma za su zama ƙari ga kokarin ganin an samu zaman lafiya.
Da yake magana, wani dattijon jam’iyar Ali Maiunguwa Musawa ya ce jam’iyar ta AA zata samar da ilimi da shirye shiryen bunkasa rayuwar al’umma kyauta ga matasa da mata don ganin an taimaka masu.
Tunda farko, saida dan takarar gwamnan jam’iyar Garba Sani Dankane ya yi alƙawarin tafiyar da gwamnatin shi da kowa da kowa don ciyar da jihar gaba.
Garba Sani Dankane ya bukaci mutane su zabi jam’iyar AA, tare da cewa zata kawo sauye-sauyen da ake bukata a jihar Katsina idan ta lashe zabe.
Abubuwan da suka gudana a wurin sun hada da bada gudunmawar sama da naira miliyan 40 daga Barrister Mai-Nasara Umar Kogo, Dahiru Magaji Jikamshi, Ibrahim Na-Kaduna Jikamshi da kuma ƙananan hukumomin shiryar Funtua 11.
