Wasu Al’ummomin Jihar Katsina Sun Bukaci A Cika masu Alƙawarin Samar Da Tallafi Ga Mutanen Da Ayyukan Ta’addanci Ya Shafa.
Al’ummomin garin Guga dake cikin karamar hukumar Bakori sun yi tunin ganin gwamnatin jihar Katsina ta cika masu alƙawarin samar da tallafi ga wadanda ayyukan ta’addanci ya shafa a yankin.
Mai magana da yawun al’ummomin yankin Wada Guda ya ce mafi akasarin mutanen da aka sako bayanda yan ta’adda suka yi garkuwa da su yanzu basu da sauran abun ci gaba da harkokinsu.
Kamar yadda ya bayyana, yan ta’addan sun kashe al’ummomin garin Gugar da dama, tare da ja masu asarar dukiyoyi a cikin shekarar da ta gabata.
Ya ce gwamnatin jiha ta kafa kwamitin da zai tattara sunayen mutanen da abun ya shafa, amma har yanzu babu abinda aka yi akan batun.
Sannan ya yi kira ga hukumar kula da hanyoyin jihar Katsina ta sake shinfida hayar Bakori-Guga-Kakumi domin saukaka harkokin zirga-zirgar yankin, masamman ma na gona.
