September 18, 2026

Sarkin Katsina Ya Buƙaci Mutane Su Ci Gaba Halaye Masu Kyau Bayan Ramadan.

0

Daga Auwal Isah

Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya bukaci alumma da su yi aiki domin cigaban addinin Islama.

Alhaji Abdulmumin kabir usman ya bayyana hakan ne a garin Rimi a lokacin rufe tafsirin alkur’ani mai tsarki na wannan shekarar a fadar Kauran KT hakimin Rimi.

Sarkin ya kuma bukaci masu hannu da shuni dasu tabbatar cewa suna bada zakka akan lokaci domin bunkasa rayuwar masu karamin karfi a cikin alumma.

Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya kara da jaddada bukatar cigaba da kyawawan ayyuka bayan Ramadan.

Kauran Katsina Alhaji Nuhu Abdulkadir da Maji dadin Katsina hakimin Tsagero sun godema sarkin bisa samun lokaci domin shaida rufe tafsirin na watan ramadan din a Rimi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *