November 17, 2026

An Raba Buhunnan Abinci 431 A Katsina

0

Daga Auwal Isah

Karamar hukumar Rimi ta raba buhunan masara 431 ga alummar yan’kin.

Shugaban Karamar hukumar Alhaji Lu’uman Muhammad Imam wanda ya kaddamar da rabon masarar a Rimi ya bayyana godiyarshi ga gwamna Aminu Bello Masari bisa Samar da tallafin.

Alhaji Lu’uman Muhammad ya bukaci kwamitin rabon masarar da ya saka gaskiya wajen rabon kayan.

Shugaban Karamar hukumar ta Rimi ya bayyana jin dadinshi ga dukkan masu ruwa da tsaki bisa rawar da suka taka a lokacin zaben kananan hukumomi da ya gudana a yankin.

A jawabin maraba, shugaban jam’iyyar APC na mazabar Rimi Ibrahim kwayo da kuma shugabar mata hajiya Sahura Muhammad sun bada tabbacin raba kayan bisa gaskiya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *