September 19, 2026

Sanata Sahabi Liman Ya Nemi Goyan Bayan Mazaɓarsa A Zaɓen 2023

0

Daga Hussaini Ibrahim

Dan takarar Majalisar Dattawa, ƙarƙashin jami’yyar APC mai ya wakiltar Zamfara ta Arewa Sanata Sahabi Yau Kauran Namoda ya nemi goyan bayan al’ummar Mazaɓarsa na komawa kujerar Sanata a zaɓe mai zuwa .

Sanata Sahabi Yau Kauran Namoda ya bayyana haka a wajan ƙaddamar da yakin neman zaɓensa a zaɓen shekarar 2023 a ƙaramar hukumar Kauran Namoda.

A jawabin nasa Sanata ya bayyana ayyukan da ya kawo na cigaba a yankin nasa da kuma mutanan da suka amfani wajan samar masu ayyuka na gwamnatin Tarayya.da kuma tallafin da ya ke badawa wajan ilimi da koyan sana’a a mazaɓarsa.

Kuma ya bayyana yadda ya ke hurawa gwamnatin Tarayya wuta wajan kawo ƙarshen ‘yan bindiga da suka addabi yankunan na su.

Akan haka ne Sanata Sahabi Liman ya tabbatar wa al’ummar mazaɓarsa cewa, Idan suka zaɓe shi ya koma majalisar Dattawa dan cigaba da wakiltar su lallai ya tabbatar masu da cewa, zai ninka ƙoƙarinsa wajan kare muradinsu da cigaban yankin ta kowane sashe inji Sanata Sahabi

A nasa jawabin shugaban yakin neman zaɓen Sanata Sahabi Liman, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Hon Mamuda Aliyu Shinkafi ya yi kira ga al’ummar mazaɓar Zamfara ta Arewa da kada suyi zaɓen wanda ba’a gwadashi angani ba kunga amfanin Sanata Sahabi Liman a gidajan ku wajan matanku da ‘ya’yan ku kayan koyan sana’a da a a horar da su kuma aka ba su kaya kyauta dan dogaro da kansu .

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *