Sanata Hadi Sirika Ya Faɗi Wurare Uku Da APC Zata Iya Cin Zaɓe A jihar Katsina
Ƙaramin ministan sufuri Sanata Hadi Sirika ya bayyana wasu wurare da yake ganin jami’yyar APC tana da karfin da babu wanda zai kada ita zaɓe mai zuwa.
Sanata Hadi Sirika yana wannan bayani ne a lokacin da bikin ƙaddamar da bada gudunmawa ga ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar APC Dakta Dikko Umar Raɗɗa da aka yi Sharaton Hotel a Abuja.
Kalaman dai na minista kamar maida martani ne ga wani ko wasu ‘yan siyasa na Katsina inda har ya yi ikirarin cewa sun tara kuɗi kuma suna da kuɗin da za su iya cin zaɓe.
“Ni naga yadda za a yi a kada Sanata Abu Ibrahim a Musawa ko a Kada Hadi Sirika a Dutsi ko kuma a kada Aminu Bello Masari a Kafur naga yadda za a yi haka.” In ji shi.
Wasu na ganin cewa jami’yyar APC ta yi rawar ganin da zata iya cinye wasu ƙananan hukumomi ba wai guda uku kawai ba. Kuma su ɗin ma ya alakanta nasarar su ne da wasu manyan mutane na ƙananan hukumomin.
Waɗannan kalaman na Sanata Hadi Sirika na zuwa ne a daidai lokacin da jami’yyar APC a jihar Katsina da matakin ƙasa ta ƙaddamar da yakin neman zaɓe ta wani irin salo na ban hakuri ga jama’a.
Sai dai kuma masana na ganin cewa mutum kamar Sanata Hadi Sirika ya riƙa yi wa duniya ikirarin cewa sun tara kuɗi suna da kuɗi ba daidai bane a siyasa.
Haka kuma wasu na sokar sa da cewa mutumin da ya tsame hannunsa daga al’amarin siyasar jihar Katsina baƙi ɗaya kuma yanzu yake irin wadanda kalaman, kosai shima ya dawo tafiyar ne tsakani da Allah.
