September 18, 2026

Sallah: Gwamna Dauda yayi kira ga Zamfarawa da su Ƙara hakuri da yin addu’ar samun Nasara ga gwamnati sa

0

Daga Hussaini Ibrahim

Gwamman Jihar Zamfara,Dauda Lawal yayi kira ga al’ummar Jihar Zamfara, da su kara hakuri akan mawuyacin hali da ake ciki da kuma yin addu’ar samun zaman lafiya a lokotan bokukuwan Sallah .

Dauda Lawal ya bayyana haka ne alokacin da ya ke gabatar da Jawabin barka da Sallah babba watau Edil Kabir fadar gidan gwamnati da ke Gusau.

A jawabin sa ya bayyyana cewa,yau bamu wuce wata guda ba da amsar mulki kuma gashi mun samu Jihar cikin mawuyacin hali na rashin tsaro, ta barbarewar Ilimi, matsalar ruwan sha da ta’adabi Gusau da sauran Kananan hukumomi a yanzu haka.

Cikin taimakon Allah yanzu mufara shawo kan matsalar ruwan sha na Gusau,kuma da yardar Allah sauran Kananan hukumomi ma zamu san abunyi akan su dan magance matsalar ruwan sha.

Gwamna Dauda Lawal ya mika godan Sallah ga Zamfarawa na albishir din magance matsalar da ake ciki da fatan zamuyi bukukuwan Sallah Lafiya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *