September 18, 2026

PTA Ta Yaba Ma Gwamnan Jihar Katsina Bisa Naɗe-naɗen Da Yayi Masamman Ma A Hukumar SUBEB.

0

Kungiyar iyayen dalibai wato PTA a takaice ta yaba ma gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda bisa naɗa shugabannin hukumomin, ma’aikatu da kuma sassan gwamnatin bisa cancanta, masamman ma a hukumar bayar da ilimin bai ɗaya ta SUBEB.

Kungiyar iyayen ɗalibai reshen ƙaramar hukumar Katsina ta yi wannan yaban a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Malam Abubakar Aliyu Alkasim Farin Yaro ya fitar.

Shugaban kungiyar ya ja hankalin sabon shugaban hukumar Dr. Kabir Magaji Gafia ya maida hankali wurin ganin an rage cunkoson dalibai a cikin azuzuwa, ya tabbatar da ganin an ida gyare-gyaren sauran makarantun da ba’a ida, tare da yin kira ga Sabon shugaban da ya himmatu wurin kyautatawa malamai masu kwazo.

Ya bukaci a samar da kayan koyo da koyarwa isassu a makarantun firamare dake fadin jihar Katsina, sannan a cigaba da bin hanyoyin horar da malamai domin inganta koyo da koyarwa.

Malam Abubakar Aliyu Alkasim Farin Yaro ya ƙara yin kira ga shugaban da ya zamo mai yawaita kai ziyarar gani da ido a makarantun firamare dake fadin jihar Katsina tare da sauraren koken Shuwagabannin Makarantun firamare (Hedimastoci).

Hakanan kuma wannan ƙungiya na ƙara godiya ga sakataren ilmi na ƙaramar hukumar Katsina da Ma’aikatanshi bisa jajircewarsu ga aiki.

Daga nan sai kungiyar ta yaba ma Dikko Umaru Radda bisa matakan da ya dauka akan ilmi, tare da yi gwamnatinshi addu’ar samun nasara

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *