Sabbin Jarumai Basa Samun Damar Da Ya Kamata A Kannywoo. Cewar Safna Lawan
Jaruma a masana’antar Kannywood ta nuna takaicin ta a game da rashin samun dama da ƙananan Jarumai suke yi a cikin Masana’antar Kannywood ba kamar yadda harkar take ba a Hollywoow da Bollywood.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar ta da wakilin mu in da take cewa ” Yanzu kamar a Indiya ne. Idan ƙaramar jaruma ta shigo za su yi yadda za su yi ne su sa duniya ta san ta har a yi alfahari da ita. To a nan ne za a gane kwarewar ta.
Don haka abin da ya kamata a rinƙa yi wa ƙananan jarumai Idan sun shigo Kannywood a rinƙa ba su sin ɗaya biyu a cikin fim ko da kuwa kurman sin ne a nan za a ga kwarewar sa har a ba shi babban fim, to a gaskiya muna da ƙarancin wannan ga kuma jarumai mata ɗin mun yi yawa don haka ya kamata a duba wannan matsalar.”
Dangane da nasarorin da ta samu acikin wannan harkar ta fim kuwa cewa ta yi.
“A gaskiya na samu nasarori da yawa domin na shiga manyan finafinai kamar Laure da Izzar so, Ina da Buri sannan na samu damar shiga fim din Sarah.”
Safna Lawan ta ci gaba da cewa
“Daman tun ina ƙaramar nake da burin shiga harkar fim domin ina son na faɗskar da jama’a da jama’a kuma a yanzu ga shi na samu dama, don haka a yanzu babban burin da nake da shi na ga na samu zama babbar jaruma da duniya ta san da ita, don haka ina fatan Allah ya cika mini burin da nake da shi.” Inji Safna Lawan.
