September 16, 2026

Rikicin PDP: Wike Ne Kansar Da Ta Hana PDP Zaman Lafiya A Nijeriya -Mustapha Inuwa 

0

Rikicin PDP: Wike Ne Kansar Da Ta Hana PDP Zaman Lafiya A Nijeriya -Mustapha Inuwa

Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina ta zargin tsohon gwamnan jihar River kuma ministan birnin tarayyar Abuja Nyensom Wike da ta zama kanwa uwar gamin hana jam’iyyar zaman lafiya.

Daraktan yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar a zaɓen 2023 kuma jigo a PDP Mustapha Inuwa ne ya bayyana a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da suke yi a Katsina.

Haka kuma jam’iyyar ta ce duk inda ake samun wata rashin fahimta a jihohi da kuma kasar baki ɗaya to tsohon gwamnan jihar River ne Nyensom Wike

Mustapha Inuwa ya ƙara da cewa irin yadda aka hana wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP su sayi fom din takarar shugabancin jam’iyyar da ke tafe ya nuna cewa akwai masu mata zangon ƙasa daga matakin tarayya

A cewar Mustapha Inuwa abin ya fito fili lokacin da tsohon gwamnan jihar Bunue Samuel Ortom ya bayyana cewa shi da Wike basu da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 sai Tunibu a matsayin su na ‘yan jam’iyyar PDP.

” Hakan ta sa suke tura mutanen su duk inda za a yi zaɓen shuwagabannin jam’iyyar PDP domin su kawowa jam’iyyar cikas a lokacin zaɓe mai zuwa, kuma shine abinda suke don cimmawa

Idan za a yi tunawa jam’iyyar PDP a jihar Katsina tana fama da rikici tun bayan kammala zaɓen 2023 inda har yanzu ana cigaba da samun matsaloli abinda wasu ke ganin cewa wike ne kanwa uwar gamin wannan matsala.

Haka a matakin jihar Katsina wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar sun zargin tsohon ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023 Sanata Yakubu Lado ƊanMarke da yin uwa makarɓiya akan lamurran jam’iyyar PDP.

Kazalika Sanata Yakubu Lado na biyayya ne a bangaren tsohon gwamnan jihar River Nyesom Wike. Yanzu dai jira a gani lokacin zaɓen shuwagabannin jam’iyyar PDP da ke tafe.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *