September 18, 2026

RASUWAR EDITAN RADIYO FRANCE GARBA ALIYU TA GIRGIZA JAMA’A

0

RFI Hausa na bakin cikin sanar da rasuwar daya daga cikin ma’aikatan ta, Garba Aliyu Zaria, wanda kafin rasuwar sa yake rike da mukamin Mataimakin Edita.

Garba ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin lafiya bayan ya gabatar da shirin safe jiya asabar 05 ga watan Fabarairu.

Marigayin ya bada gudumawa sosai wajen ci gaban da RFI Hausa ta samu a shekarun da ya kwashe yana aiki.

Za’ayi janaizar sa yau da safe a unguwar Agege dake birnin Lagos.

Da fatan Allah Ya gafarta masa, Ya kuma masa Rahama.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *