Jam’iyyar PDP Na Cigaba Da Neman Hadin Kan ‘ya ‘yanta Domin Samun Nasarar Zaban Kananan Hukumomi A Katsina
Shugaban Jam’iyyar PDP ta jihar katsina Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya halarci zaɓen yar tunke (kato bayan kato) Na neman takarar kansila da zaɓen wakilai ukku na musamman na mazabar sabuwar rijiya karamar hukumar Mashi
Wannan ziyara dai na daga cikin gwaji da kuma shirye-shiryen zaɓen kananan hukumomi da za’ayi a jihar Katsina
Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya yi kira ga ya’yan jam’iyyar ta PDP da su hada kan su musamman ma yanzu da ake tunkarar zabukan kananan hukumomi da mazabu na jihar Katsinaatsina.
Ya kuma Kara jadadaal bukatar da ake da ita da suyi biyayya ga wanda Allah yaba ikon chinye wannan zaben kansila na sabuwar rijiya wato Hon. Bilyaminu Usman
Kamar yadda Rahotanni suka bayyana an gudanar da wannan zabe lafiya an kuma tashi lafiya.
