September 17, 2026

NLC: ƙarin Farashin Man Fetur Zai Kashe Mutane Da Dama

0

Daga Awwal Isah, Katsina

Shugaban ƙungiyar kwadago na Nigeria Ayuba Wabba ya ce shirin ƙara farashin man fetur da ake yi zai yi sanadiyar mutuwar ƴan Najeriya da dama da wuri.

Majiyar mu ta jaridar “The Cable” ta bada rohotan cewa, akwai yiyyiwar gwamnatin tarayya ta ƙara farashin litar man fetur zuwa 30 nan da zuwa watan mai kamawa na Fabarairu, idan dai har aka aiwatar da shawarwarin kwamitin wucin gadi na ƙasa akan tattalin arzuƙi.

Ministar kuɗi da tsare tsaren ƙasa Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya za ta iya biyan kuɗin tallafin man fetur na watanni 6 ne kaɗai a wannan sabuwar shekarar ta 2022 da muke ciki.

Kuma wannan sanarwar ta ci gaba da haifar da maida martani a tsakanin ‘ƴan Najeriya, inda ma ƙungiyar kwadago ke barazanar tafiya yajin aiki, idan dai har gwamnatin tarayya bata sauya wannan matsayar ba.

Da ya ke magana a kan wannan batu ranar Alhamis a gidan talabijin na “Channels” Ayuba Wabba ya jajirce cewa,  ƙungiyoyin kwadago ba za su amince da wannan ƙarin kuɗin man ba.

Inda ya ce a shekarar 2016, sun yi alƙawalin aiwatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi, tare da cewa za a biya kowa da kowa. Amma har ya zuwa yanzu, jahohi 6 ba su aiwatar da tsarin ba. Kuma yana cikin alkawalin da mukai da su.

Akan batun tallafi a lokacin ɓarkewar cutar Corona kau, ya ce sun tattauna akan naira biliyan 500 da aka ware don raba ma mutane, amma shiru suke ji.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *