September 17, 2026

Budadiyar Wasika Zuwa Ga Malam Abdallah Gadon Kaya, Kano

0

Muhammad Fatuhu Mustapha

Bayan gaisuwa tare da girmamawa, ina maka sallama irin ta addinin Musulunci. Ina fata zaka kalli wannan wasika da idon basira, domin ina da tabbacin za ta yi maka da al’ummar musulmi baki daya amfani.

Zan fara da sanar maka ni ba mabiyin darikar salafiya bane, amma kuma ina ganin girman malamai, saboda ina sane da irin rawar da kuke takawa, wurin yada ilmin addinin Islama. Sai dai kash! Na lura ana neman ayiwa abin gyaran gangar auzinawa, ko kuma ana neman garin gyaran gira a rasa ido.

Ina so ka sani cewa, muhimmancin malami a al’umma a yau, a kuma Arewacin Nigeria, a wurin talaka ya wuce muhimmancin dukkan wani mai rike da madafun iko a kasar nan. Domin kuwa mabiyan ka da masu sauraron ku, suna ganin duk abinda kuka fada to kawai umarni ne daga Allah. Don haka ba su da wani zabi illa su bi.

Dan haka ya kamata malamai irin ka da suke da dimbin mabiya da masu saurare su ringa taka-tsantsan wurin maganganun su.

Maganganu biyu da kayi sun bani mamaki, kuma a gaskiya ban zace su daga gurin ka ba;

Na farko dai, kusan shekara guda da ta wuce, an jiyo ka kana bada labarin wani ya gaya maka cewa, ana zina a cikin sinima ta Film House dake katafaren shagon nan na Shoprite. Ina ganin a kaida kafin ka bayyana wannan magana ya kamata ka bincika, ka tabbatar da cewa haka ne, kuma ka nemi masu wajen ka sanar da su, domin su dau mataki wurin hana wannan mummunar dabi’a.

A matsayina na kolo a karatun addini, ni kaina nasan yadda Musulunci ya tsaurara shaidar zina, ya kuma dau mataki tsattsaura akan wanda zai bayar da shaidar zina. To amma sai naga kayi amfani da shaidar mutum daya, wanda nayi imanin ba zai iya tsayawa a gaban sharia ya kare kan sa ba. Ni ina ganin ya kamata irin wadannan labarai da ake kawowa malam, ya ringa kallon su da idon basira.

Amma babban abinda ya tayar min da hankali shi ne, maganganun ka da naji akan kisan Haneefa. Inda ka yi kira da a kashe shi wannan mugun iri da ya aikata wannan mummunan abu. Abin tsoron shi ne, a fahimtata kira kayi ga mutane da su kashe wannan mutum, wanda ni a ganina bai kamata malami kamar ya yi kalaman tunzura mutane da su dau hukunci a hannun su ba.

Na so ace kira kayi ga gwamnati da ta dau mataki cikin gaggawa ta aika da wannan mutum kotu, kuma kayi kira ga alkalai da su gaggauta shari’ar su yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata.

Illar irin wannan kira naka shi ne, in ba ayi a hankali ba, in har kowa zai dau matakin doka a hannun sa, to wata rana za a haifa dan da ba ido. Domin koda neman budurwa ya hada mu da mutum in naga zai kasa ni, zan iya tunzura mutane akan sa, su halaka shi.

Ko shakka babu  tsarin sharia Nigeriya tsari ne mai wahala da kuma murde-murde acikin sa. Wanda hakan ya sa, yanke hukunci ke da matukar wahala. Hakan ya sanya mutane da yawa sun yanke tsammanin samun adalci daga irin wannan tsari. To amma duk da haka, da babu wawa, gara da wawa. Ko ba komai tsarin dai, yana rage yawan aikata laifuka, kuma a karshe komai daren dadewa zai yanke hukunci. Kila baka san lokacin da akayi shariar Sahalatu ba a Kano, wacce ta bankawa mijin ta wuta a sakamakon zai mata kishiya.

Amma shekara biyu baya, Sahlatu ta gama zaman ta na gidan yari ta fito. Wannan na nuni da cewa, koma ina aka je aka dawo, a barwa sharia aikin ta shi ne abu mafi amfani a cikin al’umma. Sarkin Zazzau Kwasau ya taba yanke hukunci cikin gaggawa, kuma har ya mutu yana da na sani.

A nunawa al’umma muhimmancin son juna, da kyakkyawar muamala da biyayya ga shugabanni shi ne abinda zai tserar da wannan yanki namu daga fitinar da ya samu kansa ta kashe kashe da zubar da jini a tsakanin al’umma.

Ina fata Malam zai kalli wannan budaddiyar wasika tawa da idon basira.

Allah Ya karawa Malam lafiya da nisan kwana da imani.

Wasalam

Muhammad Fatuhu Mustapha marubuci ne, kuma tsohon Editan Jaridar Manhaja ta Kamfanin Blueprint da ke fitowa duk sata

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *