September 17, 2026

National Movement For Rebuilding Nigeria Ta Sallama wa Hon. Sani Aliyu Ɗanlami (Mai Raba Alheri)

0

Sananniyar kungiyar nan mai rajin sake gina Najeriya wato National Movement for Rebuilding Nigeria ta sallamawa tafiyar ɗan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya Hon. Sani Aliyu Ɗanlami mai raba alheri.

Shugaban kungiyar ta ƙasa reshen jihar Katsina, Ambassador Abubakar Matazu ya bayyana haka a lokacin da suka kaiwa ɗan takarar ziyarar ban girma a ofishin yakin neman zaben sa.

Ambassadors Abubakar ya ce mun ga cancantar Hon. Sani Aliyu Ɗanlami shi yasa suka zo su bayyana goyon bayan su a wannan tafiya ta shi domin samun nasarar zaɓe mai zuwa.

Sannan ya ɗauki alƙawarin shiga lungu da sako domin neman goyon baya jama’a su zaɓe Hon. Sani Aliyu Ɗanlami a ƙarƙashin jam’iyar APC mai alamar tsintsiya a zaɓan 2023.

A nashi ta’aliki ɗan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya Hon Sani Ɗanlami ya ce ya ji daɗin wannan ziyara ta wannan kungiyar mai rajin sake gina Najeriya.

Haka kuma ya ƙara bada tabbacin cigaba da samar da ayyukan yi musamman ga matasa waɗanda da su ne ake wannan hidima ta siyasa ba dare ba rana.

Hon. sani Aliyu Ɗanlami ya ce idan aka bashi dama ta hanyar zaben sa zuwa majalisar tarayya zai ruɓanya ƙoƙarin sa akan wanda yake yi wajan ganin an samu wakilci na gari a ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *